PDP ta kaddamar da yakin Neman Zabe a Ganjuwa


Jam'iyar PDP rashen karamar hukumar Ganjuwa ta kaddamar gangamin takara a garin Kafin- Madaki a ranar Alhamis.
Sanata Bala Adamu ke jawabi a sakatariyar PDP a Kafin-Madaki 

Taron ya samu hallatar dubban magoya bayan jam'iyar tare da shugabannin ta na Jiha, shiyya, kananan hukumomi da gundumomi. 

Tsohon sanata mai wakilatar Bauchi ta tsakiya Alh Bala Adamu Kariya ne ya jagoranci tawagar zuwa fadan maigirma Madakin Bauchi Dr. Baba Muhammad Gidado don  gaisuwan ban girma da neman albakan iyaye kasa sarakunan gargajiya.

 
Dan Takarar kujerar majalisar tarrayya mai wakilatan mazabar Ganjuwa/Darazo, Ibrahim Galadima ya halarci gangamin.
A gefe daya kuma Alhaji Yahaya Muhd Miya da Alhaji Adamu Manu Soro 'yan takarar kujerun majalisun dokokin jiha Ganjuwa ta Yamma da ta Gabas.

Har ila yau Shugaban Jam'iyar PDP na shiyyan Bauchi ta tsakiya Hon.Nuhu Zaki ya halarci gangamin. 

Post a Comment

0 Comments