APC ta yi gangami a Kafin-Madaki

Jam'iyar APC rashen karamar hukumar Ganjuwa ta kaddamar gangamin takara a garin Kafin- Madaki a ranar Jumma'a.


Taron ya samu hallatar dubban magoya bayan jam'iyar tare da shugabanta na karamar Hukuma Ibrahim Kafin-Galadima  da shugabannin na  gundumomi.
Dan takarar sanata mai wakilatar Bauchi ta tsakiya Hon Halliru Dauda Jika ne ya jagoranci tawagar zuwa fadan maigirma Madakin Bauchi Dr. Baba Muhammad Gidado don  gaisuwan ban girma da neman albakan iyaye kasa sarakunan gargajiya.

Dan Takarar kujerar majalisar tarrayya mai wakilatan mazabar Ganjuwa/Darazo, Mansur Manu Soro ya halarci gangamin.
A gefe daya kuma Engr Yusuf Inuwa Dadiye a da Garzali Abubakar 'yan takarar kujerun majalisun dokokin jiha Ganjuwa ta Yamma da ta Gabas.

Post a Comment

0 Comments