Hotuna:Wani tsohon massallaci ne Masarauta Bauchi ke girmamawa?

Masarautar Bauchi tana girmama wani masallaci mai dogon tarihi da ke Gilliri a cikin karamar Hukumar Ganjuwa.

Masana tarihi sun bayyana cewa ya kai kimanin shekara sama da 400.

Wakilin tarihin Bauchi, Alhaji Ado Dan Rimi yace " masallacin malam Abdullah kakan malam yaqubu mai shekaru Sama da dari hudu bai rushe ba a garin Gilliri''.

Daga lokaci zuwa lokaci Sarakunan Bauchi kan ziyarci masallacin don yi addu'oi da sallah.

Ga wasu hotuna yayin ziyarar Sarkin Bauchi (Dr) Ridwan Sulaiman ya ka masallacin.

Hakkin mallakan Hotuna: Wakilin Tarihin Bauchi 


Post a Comment

0 Comments