Facebook ya yi sanadin hada aure a Nijeriya - Arewa Affairs

Thursday, 11 January 2018

Facebook ya yi sanadin hada aure a Nijeriya
Wani dan Najeriya ma'abocin shafunkan sada zumunta ya yi aure cikin mako daya bayan tallata kansa a shafinsa na Facebook.


Chidinma da Amaryansa Sophy Ijeoma 

A ranar Asabar 30 ga watan Disambar shekarar 2017 ne Chidimma Obodoechina Amedu ya bayyana bukatarsa ta neman matar da zai aura.
"Shekaruna sun kai kuma a shirye nake na yi aure ba tare da bata lokaci ba. Za ku iya turo min da bukatarku. Wadda ta yi nasara za a daura mana aure da ita ranar 6 ga watan Janairu. Zan rufe karbar sunaye karfe 12 na daren ranar 31/12/2017."
"Da gaske nake fa, kada ku ce ba ku gani ba a kan lokaci. Allah Ya ba da sa'a," in ji shi.
Daga nan sai dumbin mutane suka fara bayyana ra'ayoyinsu game da batun, ciki har da wadansu daga cikin 'yan matan da suka amince da bukatarsa.
Chidimma ya ce bayan tantance dimbin 'yan matan da suka bayyana sha'awarsu, sai ya zabi guda.
Saurayin ya ce ya gana da mahaifin yarinyar a ranar 1 ga watan Janairun bana.
A ranar Asabar 6 ga watan Janairu ne aka daura auren Chidimma da amaryarsa Sophy Ijeoma wadda ya samu daga shafin Facebook.

No comments:

Post a Comment


offeroffer
Do You Love The Current Design Of This Blog? We Can Set Up Same Design For You At An Affordable Price.

Click Here Now To Get Started!


HOME | ABOUT | CONTACT US | ADVERTISE | PRIVACY POLICY
DISCLAIMER

Copyright © 2019. Powered by Arewa Affairs.