Ko kun san Beraye na aikin likitoci? - Arewa Affairs

Friday, 15 December 2017

Ko kun san Beraye na aikin likitoci?
Cigaban kimiyya da fasaha kuma da abubuwan mamaki basu karewa a duniya, a kasar Tanzania tana kokarin rubanya yawan berayen da take horas da su wajen sansano kwayar cutar tarin fuka wato TB saboda yadda suke da saurin gano ta.

Su dai berayen an horas da su ta yadda za su gano cututtuka masu halaka jama'a ta hanyar sunsuna majinar mutane.
Haka kuma cikin minti 20 kacal, berayen za su iya sunsuno majinar mutane 100, wanda sai jami'an kiwon lafiya masu aiki a dakunan binciken cututtuka sun kwashe kwanaki hudu kafin su iya yin haka.
yanzu dai Tanzania za ta yi amfani da berayen a wasu kananan asibitoci 60 a fadin kasar.
Kusan shekara goma da ta wuce ne wata gidauniya da ke kasar Belgium ta fara amfani da berayen saboda saukin kudi da kuma sauri da suke da shi wurin aikin idan aka kwatanta da ainahin hanyoyin da aka saba bi wajen gwaji don gano kwayar cutar ta tarin fuka.
Kasar Tanzania dai na cikin kasashe 30 da ake ganin sun fi fama tare da yada cutar ta tarin fuka, wadda tana daya daga cikin cutukan da suka fi hadari a duniya, kodayake ana maganinta da rigakafinta.

Hakkin mallaka: BBC Hausa 

No comments:

Post a Comment


offeroffer
Do You Love The Current Design Of This Blog? We Can Set Up Same Design For You At An Affordable Price.

Click Here Now To Get Started!


HOME | ABOUT | CONTACT US | ADVERTISE | PRIVACY POLICY
DISCLAIMER

Copyright © 2019. Powered by Arewa Affairs.